Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League

 

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League

Chamiopns League

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Real Madrid da Manchester City za su fafata a wasan daf da karshe a Champions League ranar Talata a Santiago Bernabeu.

Real Madrid ta kawo wannan matakin, bayan da ta yi waje da Chelsea da cin 4-0 gida da waje, tun kan nan ita ce ta fitar da Liverpool.

City kuwa ta yi nasarar doke Bayern Munich da cin 4-1 gida da waje, bayan da suka tashi 1-1 ranar Laraba a Jamus a wasa na biyu a quarter finals.

Hakan ne ya sa Real Madrid mai rike da Champions League na bara mai 14 jimilla za ta kece raini da City, wadda ba ta taba lashe kofin ba.

Manchester City ta zama ta uku daga Ingila da ta kai daf da karshe a kaka uku a jere a Champions League, bayan Chelsea da Manchester United.

Kawo yanzu Erling Haaland na Manchester City ya ci kwallo 12 a Champions League, shine kan gaba a wannan kwazon,

Yayin da Vinicius Junior na Real Madrid keda shida a raga kawo yanzu.

A kakar bara Real Madrid ta fitar da City a daf da karshe da cin 6-5 gida da waje, bayan da kungiyar Sifaniya ta fara rashin nasara 4-3 a Etihad, amma ta ci 3-1 a Santiago Bernabeu a karawa ta biyu.

Real Madrid da Manchester City sun kece raini sau takwas a Champions League, kowacce ta ci karawa uku-uku da canjaras biyu.

Sun fara wasa a tsakaninsu ranar Talata 12 ga watan Satumbar 2012, inda Real ta yi nasarar cin 3-2.

Wasa tsakanin Real Madrid da Manchester City:

Champions League Laraba 4 ga watan Mayun 2022

  • Real Madrid 3 - 1 Man City

Champions League Talata 26 ga watan Afirilun 2022

  • Man City 4 - 3 Real Madrid

Champions League Juma'a 7 ga watan Agustan 2020

  • Man City 2 - 1 Real Madrid

Champions League Laraba 26 ga watan Fabrairun 2020

  • Real Madrid 1 - 2 Man City

Champions League Laraba 4 ga watan Mayun 2016

  • Real Madrid 1 - 0 Man City

Champions League Talata 26 ga watan Afirilun 2016

  • Man City 0 - 0 Real Madrid

Champions League Laraba 21 ga watan Nuwambar 2012

  • Man City 1 - 1 Real Madrid

Champions League Talata 18 ga watan Satumbar 2012

  • Real Madrid 3 - 2 Man City

Comments