Amfanin lemun tsami da madara

 (Gyara mai haskake fata)

    MADARA DA LEMON TSAMI


Yadda ake gyaran jiki da madara da lemon tsami.


Shi wannan hadi yana qarawa jiki kyau da kuma haske idan anayi akai akai. Yadda akeyin wannan hadi shine:

A samu madarar gari, a jika kadan da ruwa sannan sai a matse lemon tsami a ciki, a gauraya sosai sai a shafe fuska da hannu dama duk inda ake da bukatar yayi haske da laushi koda duka jiki ne za a iya shafawa. Wannan hadi idan anayinshi akai akai za aga yadda jiki xaiyi kyau, laushi da kuma haske. Bayan anshafa, sai a barshi na tsowon minti sha biyar, sannan a wanke da ruwan dumi.

✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍


  LEMON TSAMI, MADARA DA KUMA ZUMA

Shima wannan hadin ana had a shine Lamar yadda akayi wancan hadin na farko, saidai shi wannan za a kara Zuma a ciki sai a gaurayeshi sosai, sannan a shafa a barshi yayi mintuna sha Biyar(15) ko ashirin sannan sai a wanke da ruwan dumi. Shima wannan hadin yana kara kyau, haske da kuma laushin fata.bayan an wanke sai a nimi mai, kirin (cream) ba lotion ba, mai kyau da kamshi sai a shafa saboda shi lotion bays rike jiki musammama lokacin sanyi. Amma shi cream yana rike fata ya kuma sa fata tayi kyau.sosai.

✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍

sirrin rike miji

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League