Kyran jiki

 *Gyaran Jiki  Madara da lemun Tsami*


Yadda ake gyaran jiki da madara da kuma lemon tsami.


Shi wanna hadi yana qara wa jiki kyau da kuma haske idan ana yi akai akai. yadda ake yin wannan hadi shi ne:


A samu madarar gari, a jika kadan da ruwa sannan sai a matse lemon tsami a ciki, a gauraya sosai sai a shafe fuska da hannu dama duk inda ake da bukatar yayi haske da laushi ko da duka jiki ne za a iya shafawa. Wannan hadi idan ana yin shi akai-akai za a ga yadda jiki zai yi kyau, laushi da kuma haske. Bayan an shafa, sai a barshi na tsawon minti biyar, sannan a wanke da ruwan dumi.


GA JIKIN MACE 01:


🍶Shan ruwa isashe yana gyara al'auran mace. Kuma ya rinƙa gyara yanda ƙamshin sa ko ɗanɗanon sa ya ke ga mai sha🙃. Shan ruwa mai kyau mai yawa yana flushing system ɗinki, kuma ya iya fitar da infections tare ma da wasu cutuka ko wari. Rashin shan ruwa isashe zai iya haddasa miki abubuwa da yawa a jikinki kamar:


🍶a. Yawan kasala da gajiya da yawan bacci, ciwon kai, jiri, jin amai, ko jin zazzabi

🍶b. Matsewar bayan gida.

🍶c. Ciwon gaɓuɓɓu ko na jijiyoyi.

🍶d. Lalacewar fata ko ido dss.


🍶Waɗannan ƙananan matsaloli kenan. In kina shan ruwa isashe ko da futsarin ki yellow ne, ranar ko washe gari zaki ga ya koma fari qal. Don haka mata mu rinƙa ƙoƙarin shan ruwa musamman kofi ɗaya na safen nan kafin a ci komai.


sirrin rike miji

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League