Yana bani labari Yana kuka nima ina kuka

 Yana Bani Labarin Yana Kuka Nima Ina Kuka😭😭


Tunda Nai Aure Wallahi Matata Ce Take Min Wankin Kaya Na Tsahon Shekaru 20 Kenan


A Duk Tsahon Lokutannan Ban Taba Gode Mata Ba Idan Taimin Korafi Akan Hakan Sai Nace Mata Ai Ibada Kike Yi Ba Sai Nagode Miki Ba


Haka Take Hakuri Ta Rabu Dani Kuma Bata Dai Na Abinda Take Yi Ba A Wasu Lokutan Takan Nuna Min Cewa Akallah Idan Nagode Mata Zata Ji Dadi Amma Wallahi Bana Kula Ta Hasalima Fada Nake Yi Mata


Sai Nace Mata Zan Karo Aure Tunda Ita Godiya Take Bukata Sai Tayi Dariya Tace Min Ka Karo Mana Ai Ko Wacce Mace Da Halinta Zata Zauna


Idan Ta Fada Min Haka Sai Na Gwaleta Nace Kishi Ne Da Bakin Ciki Yake Damun Ta


Takan Yawan Fada Min Cewa Abban (Aisha) Ina Son Ka Bana Jin Dadin Yadda Kake Min Dan Allah Idan Nai Maka Laifi Ne Kake Min Haka Kayi Hakuri


Amma Wallahi Ko A Jiki Na


Takaici Yakan Sata Tace Min Allah Yasa Na Riga Ka Mutuwa A Lokacin Zaka Gane Irin Son Dana Ke Yi Maka A Rayuwa Da Kuma Hakurin Dana Keyi Da Kai Ina Mai Tabbatar Maka Bako Wacce Mace Ce Zata Yi Hakuri Dakai Ba


Ina Son Na Riga Ka Mutawa Domin Bana Bukatar Wani Namiji Ya Taba Jiki Na Ballantana Ya Mallake Ni A Matsayin Mata Kai Kadai Nake Burin Zama Dashi A Rayuwa Ta


Yanzu Maganar Dana Ke Yi Maka Allah Ya Dauke Kayar Sa 😭😭 Matata Fatima


Yanzu Nayi Aure Kuma Allah Ya Buda Min Kuma Na Samu Dukiya Mai Yawa Matar Dana Aura Kafin A Daura Mana Auren Sai Dana Kaita Aikin Hajji Sannan Na Siya Mata Motar Miliyan Biyu Nayi Mata Lefe Na Gani Na Fada


Abinda Yanzu Yake Damuna A Rayuwa Ta Shi Ne Duk Abinda Nayi Mata Bata Gode Min Abinda Take Nuna Min Kullum Shi Ne Hakkin Tane Kuma A Gidan Su Tana Samun Sama Da Abinda Nake Yi Mata Dan Haka Bata Bajinta Nake Yi Ba Da Zata Na Gode Min


Wallahi Abin Yana Damu Na Ita Ko Kayan Ta Bata Iya Wankewa Ballantana Nawa


Duk Lokacin Dana Yi Mata Abu Bata Gode Min Ba Sai Na Tuna Da Matata Fatima Nace Toh Daman Haka Take Jin Zafi A Cikin Zuciyar Ta Lallai Fatima Jaruma Ce.

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League