MATA KAWAI..NASIHOHI DON DAWOWA DA SOYAYYA DA RAYUWAR AURE.

 MATA KAWAI... Nasihohi don dawo da soyayya da raya rayuwar aure.


©️ Abdulhadi Aminu.


Namiji a ɗabi'a baya son mace mai nuna isa da mulkin mallaka a mafi yawan al'amuran rayuwa komai kusancinta da shi, don haka ki nisanci fifita ra'ayinki a kowanne lokaci, kuma kada ki yanke wani hukunci ba tare da neman shawararsa ba, kamar yadda masaniyar dangantakar aure Olga Francis ta bayyana a wani bincikenta.

Idan kika fahimci cewa mijinki yana yin banza da ke ko yana share ki, to kina bukatar ki yi aiki da hankali, kar ki ɗauki zargi da damuwa ki sa a ranki, haka kuma arangama da mijin a wannan lokacin ba zata haifar da ɗa mai ido ba.


Abin da ya fi dacewa ki yi shi ne:


1- Ƙoƙarin gyara kanki: Domin mace ta sabunta rayuwar aurenta ta hanya mai kyau, dole ne ta sanya lura zuwa ga gazawa da naƙasu da take da shi don samun damar magance su, wanda wannan mataki ne mai matukar muhimmanci kuma ya zama wajibi ga mai son yin rayuwa mai inganci.


2- Faɗa wa miji gaskiya: Dole ne mace ta kasance mai gaskiya ga mijinta idan har aka samu gazawa a kowane fanni na rayuwar aure, kuma ta sanar da shi burinta na sabunta rayuwar aurensu ta hanya mafi kyau, ta yi ƙoƙarin gamsar da shi cewa shi fa yana da rawar da zai taka wajen ganin rayuwar aurensu ta inganta. nasara.

Dole ne kuma ta zaɓi lokutan da suka dace don jawo hankalinsa tare da bayyana ra'ayoyinta, burinta da tunanin da ke yawo a ƙwaƙwalwarta.

Ya kamata uwargida ta tabbatar da cewa sadarwarta da mijinta a bayyane take da kyau don rage rashin fahimtar juna da karfafa amana da mutuntawa da gaskiya a tsakaninsu da kuma kara gamsuwa da junansu.


Zan ci gaba...

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League