AMFANIN KWAI WAJEN GYARAN FUSKA

 AMFANIN KWAI WAJEN GYARAN FUSKA:


🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚


kurajen fuska na daya daga cikin ababen da ke bata fuska. Akwai wadansu kuraje masu yawan naci. Ya kamata mu kula da fuskarmu musamman ma lokacin damina saboda a lokacin ne fuska takan fitar da gishiri watau a Turance ‘sebum’, kamar yadda muka sani, gishirin fuska na toshe ramukan da gumi ke fitowa. Idan hakan ya faru, sai fuska ta fara yin kuraje.


Ababen da za a bukata:


Kwanuka biyu 🍲

• kwai daya 🥚

• Takardar ‘tissue’ daya 🔵


Amfanin kwai ga fuska:


• Ruwan kwai na da sinadarin gina jiki da sinadarin bitamin da kuma ‘minerals’ 🥚

• Yana kare fuska daga kuraje.🥚

• Yana kuma rage tsufar fuska.🥚

• kara  wa fuska haske.🥚

•Rage kumburin ido.🥚


A samu kwano daya sai a zuba ruwan zafi, wanda da shi ne za a turara fuskar. Kwano na biyu kuma sai a zuba ruwan kwai bayan an cire gwaiduwar, sannan  a shafa ruwan ‘rose water’ saboda samun biyan bukata.


YADDA ZAKI HADA SHI:

🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚

•A fasa kwai sai a cire gwaiduwar.

•A kada farin ruwan kwan har sai ya yi kumfa.

• Daga nan sai a shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma a kan kurajen.


•🥚 A yagi takardar ‘tissue paper’ kadan, sai a manna a fuskar daga kan hanci har zuwa kumatu.


• A kara dora wata takardar ‘tissue paper’ a kan wanda aka manna a fuska tun a farko, watau hawa biyu kenan?


•Kada a yi dariya ko magana bayan an gama manna takardar ‘tissue paper’, domin yin hakan zai iya bude fuska, wadda kuma ana sanya takardar tissue paper din ne don ya matse fuska.

🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚🥚

• Bayan hadin ya bushe, sai a wanke fuskar.

• Sannan sai a shafa gwaiduwar kwan a fuska na tsawon minti 15, sannan a wanke.

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League