Batun Dawo Da Tsohon Sarkin Kano, Wannan Hurumin Sabon Gwamna Ne, Amma Za Mu Iya Bada Shawarar Abinda Ya Kamata, Cewar Kwankwaso

 Batun Dawo Da Tsohon Sarkin Kano, Wannan Hurumin Sabon Gwamna Ne, Amma Za Mu Iya Bada Shawarar Abinda Ya Kamata, Cewar Kwankwaso




Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi magana game da maganar shirin cire Sarkin Kano ko dawo da tsohon Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi ll.


Kwankwaso ya bayyana haka ne a yayin tattaunawar sa da ɗan jarida Abdullahi Sadou, kan batun Sarautar Kano.


An tambayi Kwankwaso kan shin da gaske ne sabon Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf zai cire Sarkin Kano tare da dawo da Khalifa Muhammad Sunusi ll.


Kwankwaso yace dama tun lokacin da muke kamfen babu abinda muka faɗawa mutane illa mun tabbatar musu cewa duk ayyukan da muka dakko su lokacin muna Gwamnati, to idan aka rantsar da sabuwar Gwamnati za'a cigaba da shi.


Kuma mu a matsayin mu na Dattawa na tafiya, za mu cigaba da basu shawarwari, domin suyi abinda ya dace.


Mun yi ƙoƙari ba mu ce za mu cire Sarki ko za'a canja ba lokacin kamfen amma yanzu kaga dama ta samu, su wadanda Allah ya bawa wannan dama su zasu zauna suyi abinda ya dace, domin mai ɗaki shi yasan inda yake masa yoyo.


Kwankwaso yace sabon Gwamnan jihar Kano zai duba ya gani, kan me ya kamata yayi kan maganar sarautar jihar Kano a halin da suka sami kansu.


Banda maganar canja sarki ma ai kunga Sarautar ma an kasata ne har kashi biyar, to duk ma dai abinda akayi zamanin gwamnatin baya, dole sai anzo anyi nazari, domin dama duk sabon shugaba yana tarar da abubuwa masu kyau da marasa kyau, masu wahalar warwarewa, amma insha Allahu Abba zai samu basirar warware abubuwa marasa kyau da aka shuka a Kano.


Kuma lallai za'a warware abubuwa yadda kowa zai sami nutsuwa, domin a cigaba da zama lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano ~ Cewar Sanata Kwankwaso

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League