EFCC ta ce Akpabio ya kai kan sa hedikwatar hukumar a ranar 9 Ga Mayu.

 Hukumar EFCC ta nemi Sanata Godswill Akpabio, kuma tsohon Ministan Harkokin Neja Delta, cewa ya bayyana domin ta bincike salwantar maƙudan kuɗaɗe a cikin aljifan sa.



Akpabio, wanda sanata ne daga jihar Akwa Ibom, ya na a sahun gaban waɗanda yanzu haka ke takarar neman zama Shugaban Majalisar Dattawa.


EFCC ta ce Akpabio ya kai kan sa hedikwatar hukumar a ranar 9 Ga Mayu.


Sanarwar ta biyo bayan wata wasiƙa da aka aika wa lauyan sa Umeh Kalu tun a ranar 13 Ga Afrilu.


Akpabio, wanda tsohon gwamnan Akwa Ibom ne, an gayyace shi a cikin watan Maris, amma sai lauyan sa Kalu ya rubuta wa EFCC wasiƙa a ranar 27 Ga Maris, ya ce Akpabio ba zai samu kai kan sa ofishin EFCC ba, saboda a ranar ya na da ganin likitan sa a ƙasar waje.


A cikin wasiƙar dai lauyan ya ƙara yi wa EFCC bayanin cewa Akpabio na fama da ciwon limoniya, kuma zuciyar sa kan fuskanci tsaikon bugawa.


Akpabio, inji lauyan sa ya na fama da matsalar yin numfashi yadda ya kamata, kuma ya na jin ciwo idan ya na numfashi, shaƙar iska na yi masa wahala.


A kan haka ne lauyan ya ce Akpabio zai iya kai kan sa ofishin EFCC bayan azumin Ramadan.


Sai dai ba a san dalilin gayyatar Akpabio shin wasu kuɗi ne ake tuhumar yasa salwantar a Ma’aikatar Harkokin Neja Delta, ko kuwa tun waɗanda EFCC ta fara tuhumar sa ne kimanin naira biliyan 108 a 2015, bayan ya kammala gwamna

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League