Ɓarayi sun yi kuskuren sace takalma duka kafar dama a wani kanti

 Ɓarayi sun yi kuskuren sace takalma duka kafar dama a wani kanti

...


Getty ImagesCopyright: Getty Images

Wasu ɓata-gari a ƙasar Peru sun yi rashin sa'a lokacin da suka je fashi a wani kantin sayar da takalma.


Mutanen uku sun fasa kantin, wanda ke a tsakiyar birnin Huancayo kuma suka kwashe takalmi sawu-ciki sama da 200, sai dai dukkanin takalmin kafar dama ne.


Mai kantin ya ƙiyasta cewa yawan takalmin da aka sace ya kai na kuɗi sama da dalar Amurka 13,000 duk da dai ɓarayin za su iya shan wahala kafin su iya sayar da su.


Kyamarorin tsaro sun nuna yadda ɓarayin suka gudanar da fashin.


Hotunan sun nuna yadda masu aikata laifin suka ɓalla kwaɗon shagon cikin tsakar dare sannan suka yi amfani da babur mai ƙafa uku wajen jigilar kwalaye maƙare da takalaman.


Shugaban ƴan sandan yankin, Eduan Daiz ya shaida wa kafafen yaɗa labaran ƙasar ta Peru cewa "Mun tattara shaidu a wurin da lamarin ya faru, abin da ba a saba gani ba game da wannan fashin shi ne an sace takalman kafar dama kawai.


"Za mu iya gano mutanen kasancewar muna da tambarin yatsunsu da kuma hotunansu."

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League