Dan Allah Bola Tinubu ka bani mukamin Ministan matasa da wasanni ~Cewar matashi Mohammad Guidance.

 Dan Allah Bola Tinubu ka bani mukamin Ministan matasa da wasanni ~Cewar matashi Mohammad Guidance.



Wani matashi Mai suna Mohammad yayi kira ga Zababben Shugaban Kasar Nageriya Bola Ahmad Tinubu da ya taimaka ya bashi mukamin Ministan matasa da wasanni na Nageriya domin samun cigaban matasan da Al'umma Baki Daya a cikin jawabin sa Yana cewa A inaso in yi amfani da wannan dama domin tunatar da mai girma Zababben Shugaban kasa Alhaji bola Ahmad tinubu kan alkawarin da ya dauka na cewa zai yi tafiya tare da matasa a Gwamnatin sa.


Duk da cewa wannan ba sabon al'amari bane ga 'yan takarar a lokacin Yakin Neman zaben daukar alkawari amma bayan yaci zabe da zarar an rantsar dashi sai Kuma ya manta da matasa abar su holoko duk da kasancewar su masu kada kuri'a fiye da kaso saba'in , kuma inaso inyi amfani da wannan dama a matsayina na matashi domin neman kujerar ministan matasa da wasanni na kasa don ganin cewa matasa ba'a barsu a baya ba domin ina da rawar da zan taka wajen cigaban matasa da kuma ciyar da kasa Zuwa mataki na gaba.


Me zaku ce?

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League