Mashaƙo ta kashe mutum 73 a Najeriya - WHO

 Mashaƙo ta kashe mutum 73 a Najeriya - WHO

Mashaƙo

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce mashaƙo ta kashe mutum 73 yayin da 557 kuma suka kamu da cutar tun fara wannan shekara.

A wani rahoto da hukumar ta fitar a jiya Laraba, ta ce an samu ɓarkewar cutar a jihohi 21 na Najeriya.

Mashaƙo dai wata cuta ce da ke kama yara waɗanda suka kai shekara biyar da kuma manya da suka haura shekara 60.

WHO ta ce an fi samun yawan alkaluman waɗand suka kamu da cutar ce a jihar Kano, inda mutum 1,118 suka kamu, sai Yobe mai 97 da Katsina mai mutum 61 da suka kamu da Legas mai 25, sai Sokoto mutum 14 da kuma Zamfara mai mutum 13.

Rahoton ya ce daga ranar 14 ga watan Mayun 2022 zuwa 9 ga watan Afrilun 2023, an samu alkaluman mutum 1, 439 da ake zargin sun kamu da cutar ta mashaƙo, inda cutar ta yi sanadiyyar rayuka 73.

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League