Takarar Shugabancin Majalisar Dattawan Nijeriya Ta Fara Daukar Zafi, Inda Za A Fafata Tsakanin Abdul'aziz Yari Da Akpabio

 Takarar Shugabancin Majalisar Dattawan Nijeriya Ta Fara Daukar Zafi, Inda Za A Fafata Tsakanin Abdul'aziz Yari Da Akpabio 



Bayan anyi zaben shugaban kasa Allah ya bawa Bola Tinubu dake kudancin Najeriya Nasara, duk da kasancewar mu bamu goyi bayan shi ba kuma bamu zabe shi ba, amma hakan baisa ranmu ya baci ba ko kuma mu cigaba da yi mishi Adawa ko hassada ba, saboda mun tabbata haka Ubangiji ya kaddara bamu isa muyi jayayya ko fada da hukuncin Ubangiji ba.  


A yanzu haka yankin Arewa ba tada wani wakilci mai karfi a cikin Gwamnatin Tarayya tunda ba tada shugaban kasa sai mataimakin shugaban kasa, shi kuma dama kusan kamar hoto ne a mulkin matukar ba shugaban kasa ne ya bashi dama a mulkin ba, kuma muna da sahihin labarin cewa Chief of Staff ma dan yankin kudu zasu bawa.


Na tabbata mukamin shugaban majalisar dattawan Najeriya ne kadai yankin Arewa za ta samu domin ta rage radadin abubuwan da suke damunta, kuma a taimaki al-ummar Arewa da mukamin.  


Mutane da dama basu san Capacity da alfarmar da kujerar ta keda shi ba, na tabbata shugaban kasa ne kadai yafi shugaban majalisar dattawan Najeriya Alfarma a Najeriya, hatta ayyuka da ake dauka a hukumomin Tarayya shugaban majalisar dattawan Najeriya yafi kowa samun dama da tsoma Mutane ta kowane fanni, a yau sabon shugaban kasar Najeriya Dan kudu ne kuma idan shugaban majalisar dattawan Najeriya ya kasance shima dan kudu na tabbata mutanan Arewa sai sun kasance abun tausayi ta kowane fanni. 


Hatta manyan ayyuka da za'a yiwa kowane yanki aiki sai shugaban majalisar dattawan Najeriya ya amince da hakan, tsayawa kai da kafa kan matsalolin da suke fuskantar Arewa matsawa fadar shugaban kasa akan yankinmu da dai sauran su. 


Duk da a yanzu haka Mutane da dama suna ganin kamar shugaban majalisar dattawan Najeriya na yanzu baida wani amfani ga Arewa tabbas kuskure ne babba, amma ba zamu gane hakan ba sai lokacin da damar hakan ta kubuce mana. 


A ranar 12 ga watan June za'a gudanar da zaben shugaban majalisar dattawan Najeriya inda tun a yanzu Bola Tinubu da jam'iyyar APC suka jaddada goyon bayan su ga Godswill Akpabio. 


Duk sauran 'yan takarar sun janye sauran Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar wanda a yanzu haka wasu da dama daga cikin Sanatotin jam'iyyar APC suke goya masa baya da kuma Sanatotin jam'iyyun Adawa na PDP, LP, NNPP, SDP, YPP da APGA. 


Sanatoti 109 ne za suyi zaben 59 na jam'iyyar APC, 36 na jam'iyyar PDP, 8 na jam'iyyar LP, 2 na jam'iyyar NNPP, 2 na jam'iyyar SDP, YPP ta nada guda 1 itama APGA ta nada guda 1. 


Na tabbata zaben shugaban majalisar dattawan Najeriya zai yi zafi sosai duba da yadda al'amuran suke tafiya. 


Nida kai mai karatu duk ba muda damar zabar wani Sanata domin ya zama Senate President, sai dai mu yiwa wanda muke fata Addu'a Allah ya bashi Nasara, Allah yasa ya zama Alkhairi ga al-ummar Arewa. 


Ni Comr Abba Sani Pantami, ina fata da burin ganin Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar ya lashe zaben wannan kujerar, domin ina masa kyakkyawar zaton al-ummar Arewa za su amfana dashi fiye da kowane shugaban majalisar dattawan Najeriya da aka taba yi.

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League