Wani saurayi ya ɓata a cikin kogo lokacin da ake sheƙa ambaliyar ruwa

 Wani saurayi ya ɓata a cikin kogo lokacin da ake sheƙa ambaliyar ruwa



Wani saurayi ya ɓata a cikin kogo lokacin da ake sheƙa ambaliyar ruwa a yankin Auckland na ƙasar New Zealand.


Matashin yana cikin ɗalibai 15 da kuma malamai guda biyu da suka tafi kogon Abbey domin ziyara.


Tun da farko, an ruwaito maƙalewar sauran ɗalibai a kogon, amma an samu damar kuɓutar da su.


Yankin Auckland, wanda shi ne birni mafi girma a New Zealand, ya ayyana dokar ta-ɓaci bayan mamakon ruwan sama da ya janyo tsayar motoci da faɗuwar itatuwa da kuma kawo tsaiko a zirga-zirgar jiragen ƙasa.


An dakatar da neman saurayin da ake yi zuwa gobe Laraba.

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League