Za mu ɓullo da matakan da za su hana alƙalai kwaɗayin cin hanci ba - Tinubu

 Za mu ɓullo da matakan da za su hana alƙalai kwaɗayin cin hanci ba - Tinubu






Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta samar da matakai da manufofin da za su sanya alƙalai da sauran ma'aikatan Najeriya daina kwaɗayin cin hanci.





Tinubu wanda za a rantsar matsayin shugaban Najeriya nan da kwana 25 masu zuwa ya ce idan aka samar da matakan ƙarfafa gwiwa da suka dace, hakan zai tabbatar da kyakkyawan yanayin aiki da manufofi da za su sanya ma'aikata cikin sauƙi su iya samu rance don biyan buƙatun rayuwa.





Hakan kuma zai rage kwaɗayin karɓar cin hanci da rashawa, in ji Tinubu.





Wata sanarwa da wani jami'i a ofishin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Abdulaziz Abdulaziz ya fitar, ta ambato cewa Tinubu ya yi wannan alƙawari ne lokacin da yake ƙaddamar da rukunin gine-ginen kotun majistare ranar Alhamis a birnin Fatakwal na jihar Ribas.





"Ba za ka yi tsammanin alƙalai su yi rayuwa a cikin yanayi maras kyawun gani ba. Wannan na cikin sauye-sauyen da suka wajaba a ƙasar nan.





Jazaman ne mu yi yaƙi da cin hanci, amma dole ne kuma sai mun yi duba a ɗaya ɓangaren. "Idan ba a son alƙalai su karɓi cin hanci, to kamata ya yi a mayar da hankali wajen kyautata jin daɗin rayuwarsu."





Zaɓaɓɓen shugaban ya ce rashin tsarin ba da rance ga masu sayen kaya, wanda zai bai wa ma'aikata damar mallakar wata kadara kamar gidaje da motoci shi ne yake ingiza su neman cin hanci da rashawa.





"Idan kana da tsarin ba da rancen sayen kayayyaki, zai iya rage kwaɗayin karɓar cin hanci. Ba ma son alƙalanmu su kaance masu sako-sako da shari'a. Na yi alƙawarin za mu yi bitar dukkan irin waɗannan manufofi."

Comments

Popular posts from this blog

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League