MATA KAWAI..NASIHOHI DON DAWOWA DA SOYAYYA DA RAYUWAR AURE.
MATA KAWAI... Nasihohi don dawo da soyayya da raya rayuwar aure. ©️ Abdulhadi Aminu. Namiji a ɗabi'a baya son mace mai nuna isa da mulkin mallaka a mafi yawan al'amuran rayuwa komai kusancinta da shi, don haka ki nisanci fifita ra'ayinki a kowanne lokaci, kuma kada ki yanke wani hukunci ba tare da neman shawararsa ba, kamar yadda masaniyar dangantakar aure Olga Francis ta bayyana a wani bincikenta. Idan kika fahimci cewa mijinki yana yin banza da ke ko yana share ki, to kina bukatar ki yi aiki da hankali, kar ki ɗauki zargi da damuwa ki sa a ranki, haka kuma arangama da mijin a wannan lokacin ba zata haifar da ɗa mai ido ba. Abin da ya fi dacewa ki yi shi ne: 1- Ƙoƙarin gyara kanki: Domin mace ta sabunta rayuwar aurenta ta hanya mai kyau, dole ne ta sanya lura zuwa ga gazawa da naƙasu da take da shi don samun damar magance su, wanda wannan mataki ne mai matukar muhimmanci kuma ya zama wajibi ga mai son yin rayuwa mai inganci. 2- Faɗa wa miji gaskiya: Dole ne mace ta kasanc