Posts

Dan Allah Bola Tinubu ka bani mukamin Ministan matasa da wasanni ~Cewar matashi Mohammad Guidance.

Image
 Dan Allah Bola Tinubu ka bani mukamin Ministan matasa da wasanni ~Cewar matashi Mohammad Guidance. Wani matashi Mai suna Mohammad yayi kira ga Zababben Shugaban Kasar Nageriya Bola Ahmad Tinubu da ya taimaka ya bashi mukamin Ministan matasa da wasanni na Nageriya domin samun cigaban matasan da Al'umma Baki Daya a cikin jawabin sa Yana cewa A inaso in yi amfani da wannan dama domin tunatar da mai girma Zababben Shugaban kasa Alhaji bola Ahmad tinubu kan alkawarin da ya dauka na cewa zai yi tafiya tare da matasa a Gwamnatin sa. Duk da cewa wannan ba sabon al'amari bane ga 'yan takarar a lokacin Yakin Neman zaben daukar alkawari amma bayan yaci zabe da zarar an rantsar dashi sai Kuma ya manta da matasa abar su holoko duk da kasancewar su masu kada kuri'a fiye da kaso saba'in , kuma inaso inyi amfani da wannan dama a matsayina na matashi domin neman kujerar ministan matasa da wasanni na kasa don ganin cewa matasa ba'a barsu a baya ba domin ina da rawar da zan ta

Ayyukan Alkairan Da Buhari Ya Gudanar A Nijeriya, Sai An Yi Shekara Dubu Ba A Samu Wanda Ya Yi Kamarsa Ba, Cewar Mai Martaba Sarkin Daura

Image
 Ayyukan Alkairan Da Buhari Ya Gudanar A Nijeriya, Sai An Yi Shekara Dubu Ba A Samu Wanda Ya Yi Kamarsa Ba, Cewar Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar

Ina Ganin Babu Wani Abin Kuskure Idan Mace Ta Fara Cewa Tana Son Namiji

Image
 Ina Ganin Babu Wani Abin Kuskure Idan Mace Ta Fara Cewa Tana Son Namiji Ni da kaina da wasu mutane kusan kaso casa'in da biyar bisa ɗari mun yarda namiji kaɗai ne ya dace idan yaga macen da yake so zai iya ya same ta ya faɗa mata babu laifi kuma ba abin kunya bane. Lokaci da dama nauyin baki na ja ma mata da yawa su kasa samun namijin da suke so wasu har ƙarshen rayuwar su. Yayin da mace ta ga wani salihi mutumin kirki ƙilan wurin aikin sune ko abokin Yayan ta ko Malamin ta ko wani abokin hulɗa namiji mutumin kirki sai ta ga kamar ci baya ne ta furta tana son sa bare tayi wani yunƙurin da zai sa ta mallake shi. Saɓanin namiji da zai iya ƙoƙarin sa domin mallakar wacce yake so idan ba a dace ba zai ƙara gaba ya nemi wata, ke ma babu inda aka hana ki, kika sani ma ko kece da kan ki za ki yi yunƙurin samun abokin rayuwa na dindin, idan ke kika gan shi kika zaɓa za ki iya jurewa a yi ta rayuwar cikin rufin asiri. Nana Khadija RA ita ta fara ganin Manzon Allah SAW tace tana son sa, suk

Wani saurayi ya ɓata a cikin kogo lokacin da ake sheƙa ambaliyar ruwa

Image
 Wani saurayi ya ɓata a cikin kogo lokacin da ake sheƙa ambaliyar ruwa Wani saurayi ya ɓata a cikin kogo lokacin da ake sheƙa ambaliyar ruwa a yankin Auckland na ƙasar New Zealand. Matashin yana cikin ɗalibai 15 da kuma malamai guda biyu da suka tafi kogon Abbey domin ziyara. Tun da farko, an ruwaito maƙalewar sauran ɗalibai a kogon, amma an samu damar kuɓutar da su. Yankin Auckland, wanda shi ne birni mafi girma a New Zealand, ya ayyana dokar ta-ɓaci bayan mamakon ruwan sama da ya janyo tsayar motoci da faɗuwar itatuwa da kuma kawo tsaiko a zirga-zirgar jiragen ƙasa. An dakatar da neman saurayin da ake yi zuwa gobe Laraba.

Shugaban 'Yan Ta'adda Mai Suna Yallow, Ya Mutu Jiya, Bayan Wata Musanyar Wuta Tsakaninsu Da sojojin Nijeriya

Image
 Shugaban 'Yan Ta'adda Mai Suna Yallow, Ya Mutu Jiya, Bayan Wata Musanyar Wuta Tsakaninsu Da sojojin Nijeriya, A Danko Wasagu Dake Jihar Kebbi

An gudanar da wani taro domin ƙaddamar da littafin da wata Bahaushiya, Dr Zainab Usman, ta rubuta kan yadda Najeriya za ta iya kauce wa ci gaba da dogaro da man fetur.

 An gudanar da wani taro domin ƙaddamar da littafin da wata Bahaushiya, Dr Zainab Usman, ta rubuta kan yadda Najeriya za ta iya kauce wa ci gaba da dogaro da man fetur.  Taron ya samu halarcin mutane da dama, a cikinsu akwai Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da Khalifan Tijjaniyya, Muhammadu Sanusi na biyu da shugaban Babban Bankin Duniya a Najeriya.  Dr Zainab Usman darakta ce a Ƙungiyar Carnegie Endowment mai nazarin al’amuran ƙasa da ƙasa da ke Amurka.

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League

Image
  Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League ASALIN HOTON, GETTY IMAGES Sa'a 1 da ta wuce Real Madrid da Manchester City za su fafata a wasan daf da karshe a Champions League ranar Talata a Santiago Bernabeu. Real Madrid ta kawo wannan matakin, bayan da ta yi waje da Chelsea da cin 4-0 gida da waje, tun kan nan ita ce ta fitar da Liverpool. City kuwa ta yi nasarar doke Bayern Munich da cin 4-1 gida da waje, bayan da suka tashi 1-1 ranar Laraba a Jamus a wasa na biyu a quarter finals. Hakan ne ya sa Real Madrid mai rike da Champions League na bara mai 14 jimilla za ta kece raini da City, wadda ba ta taba lashe kofin ba. TALLA Manchester City ta zama ta uku daga Ingila da ta kai daf da karshe a kaka uku a jere a Champions League, bayan Chelsea da Manchester United. Kawo yanzu Erling Haaland na Manchester City ya ci kwallo 12 a Champions League, shine kan gaba a wannan kwazon, Yayin da Vinicius Junior na Real Madrid keda shida a raga kawo yanzu. A kakar bara Real Madrid ta