Wa ya haifar da hargitsi a kasar Sudan? Tashin hankalin da ya abku a kasar Sudan a kwanakin nan ya ja hankalin mutanen duniya. Inda labaran da aka watsa suka nuna cewa wannan rikici ne da ake samu tsakanin shugabannin sojoji na tsagi daban daban. Sai dai idan an bi bahasin ainihin dalilin abkuwar lamarin, to, za a gano cewa, kasar Amurka da yadda take shisshigi a harkokin gidan kasar Sudan su ne suka haifar da yamutsi a kasar. Manyan jami’an da suke rikici da juna a wannan karo a kasar Sudan, wato Abdel al-Burhan, kwamandan rundunar sojojin kasar, da Mohamed Dagolo, madugun rundunar RSF, sun kwaci ikon mulki daga hannun Omar al-Bashir, tsohon shugaban kasar, ta hanyar aiwatar da juyin mulki a hadin gwiwarsu, a shekarar 2019, inda suka samu goyon baya daga kasar Amurka. Idan mun duba tarihin shisshigin kasar Amurka a kasar Sudan, za mu ga ya fara ne tun farkon mulkin shugaba Omar al-Bashir a Sudan, inda a farkon shekarun 1990, kasar Amurka ta gabatar da kara ga babban taron Majalisar