Posts

Showing posts from May, 2023

Dan Allah Bola Tinubu ka bani mukamin Ministan matasa da wasanni ~Cewar matashi Mohammad Guidance.

Image
 Dan Allah Bola Tinubu ka bani mukamin Ministan matasa da wasanni ~Cewar matashi Mohammad Guidance. Wani matashi Mai suna Mohammad yayi kira ga Zababben Shugaban Kasar Nageriya Bola Ahmad Tinubu da ya taimaka ya bashi mukamin Ministan matasa da wasanni na Nageriya domin samun cigaban matasan da Al'umma Baki Daya a cikin jawabin sa Yana cewa A inaso in yi amfani da wannan dama domin tunatar da mai girma Zababben Shugaban kasa Alhaji bola Ahmad tinubu kan alkawarin da ya dauka na cewa zai yi tafiya tare da matasa a Gwamnatin sa. Duk da cewa wannan ba sabon al'amari bane ga 'yan takarar a lokacin Yakin Neman zaben daukar alkawari amma bayan yaci zabe da zarar an rantsar dashi sai Kuma ya manta da matasa abar su holoko duk da kasancewar su masu kada kuri'a fiye da kaso saba'in , kuma inaso inyi amfani da wannan dama a matsayina na matashi domin neman kujerar ministan matasa da wasanni na kasa don ganin cewa matasa ba'a barsu a baya ba domin ina da rawar da zan ta

Ayyukan Alkairan Da Buhari Ya Gudanar A Nijeriya, Sai An Yi Shekara Dubu Ba A Samu Wanda Ya Yi Kamarsa Ba, Cewar Mai Martaba Sarkin Daura

Image
 Ayyukan Alkairan Da Buhari Ya Gudanar A Nijeriya, Sai An Yi Shekara Dubu Ba A Samu Wanda Ya Yi Kamarsa Ba, Cewar Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar

Ina Ganin Babu Wani Abin Kuskure Idan Mace Ta Fara Cewa Tana Son Namiji

Image
 Ina Ganin Babu Wani Abin Kuskure Idan Mace Ta Fara Cewa Tana Son Namiji Ni da kaina da wasu mutane kusan kaso casa'in da biyar bisa ɗari mun yarda namiji kaɗai ne ya dace idan yaga macen da yake so zai iya ya same ta ya faɗa mata babu laifi kuma ba abin kunya bane. Lokaci da dama nauyin baki na ja ma mata da yawa su kasa samun namijin da suke so wasu har ƙarshen rayuwar su. Yayin da mace ta ga wani salihi mutumin kirki ƙilan wurin aikin sune ko abokin Yayan ta ko Malamin ta ko wani abokin hulɗa namiji mutumin kirki sai ta ga kamar ci baya ne ta furta tana son sa bare tayi wani yunƙurin da zai sa ta mallake shi. Saɓanin namiji da zai iya ƙoƙarin sa domin mallakar wacce yake so idan ba a dace ba zai ƙara gaba ya nemi wata, ke ma babu inda aka hana ki, kika sani ma ko kece da kan ki za ki yi yunƙurin samun abokin rayuwa na dindin, idan ke kika gan shi kika zaɓa za ki iya jurewa a yi ta rayuwar cikin rufin asiri. Nana Khadija RA ita ta fara ganin Manzon Allah SAW tace tana son sa, suk

Wani saurayi ya ɓata a cikin kogo lokacin da ake sheƙa ambaliyar ruwa

Image
 Wani saurayi ya ɓata a cikin kogo lokacin da ake sheƙa ambaliyar ruwa Wani saurayi ya ɓata a cikin kogo lokacin da ake sheƙa ambaliyar ruwa a yankin Auckland na ƙasar New Zealand. Matashin yana cikin ɗalibai 15 da kuma malamai guda biyu da suka tafi kogon Abbey domin ziyara. Tun da farko, an ruwaito maƙalewar sauran ɗalibai a kogon, amma an samu damar kuɓutar da su. Yankin Auckland, wanda shi ne birni mafi girma a New Zealand, ya ayyana dokar ta-ɓaci bayan mamakon ruwan sama da ya janyo tsayar motoci da faɗuwar itatuwa da kuma kawo tsaiko a zirga-zirgar jiragen ƙasa. An dakatar da neman saurayin da ake yi zuwa gobe Laraba.

Shugaban 'Yan Ta'adda Mai Suna Yallow, Ya Mutu Jiya, Bayan Wata Musanyar Wuta Tsakaninsu Da sojojin Nijeriya

Image
 Shugaban 'Yan Ta'adda Mai Suna Yallow, Ya Mutu Jiya, Bayan Wata Musanyar Wuta Tsakaninsu Da sojojin Nijeriya, A Danko Wasagu Dake Jihar Kebbi

An gudanar da wani taro domin ƙaddamar da littafin da wata Bahaushiya, Dr Zainab Usman, ta rubuta kan yadda Najeriya za ta iya kauce wa ci gaba da dogaro da man fetur.

 An gudanar da wani taro domin ƙaddamar da littafin da wata Bahaushiya, Dr Zainab Usman, ta rubuta kan yadda Najeriya za ta iya kauce wa ci gaba da dogaro da man fetur.  Taron ya samu halarcin mutane da dama, a cikinsu akwai Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da Khalifan Tijjaniyya, Muhammadu Sanusi na biyu da shugaban Babban Bankin Duniya a Najeriya.  Dr Zainab Usman darakta ce a Ƙungiyar Carnegie Endowment mai nazarin al’amuran ƙasa da ƙasa da ke Amurka.

Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League

Image
  Real Madrid za ta kara da Man City a Champions League ASALIN HOTON, GETTY IMAGES Sa'a 1 da ta wuce Real Madrid da Manchester City za su fafata a wasan daf da karshe a Champions League ranar Talata a Santiago Bernabeu. Real Madrid ta kawo wannan matakin, bayan da ta yi waje da Chelsea da cin 4-0 gida da waje, tun kan nan ita ce ta fitar da Liverpool. City kuwa ta yi nasarar doke Bayern Munich da cin 4-1 gida da waje, bayan da suka tashi 1-1 ranar Laraba a Jamus a wasa na biyu a quarter finals. Hakan ne ya sa Real Madrid mai rike da Champions League na bara mai 14 jimilla za ta kece raini da City, wadda ba ta taba lashe kofin ba. TALLA Manchester City ta zama ta uku daga Ingila da ta kai daf da karshe a kaka uku a jere a Champions League, bayan Chelsea da Manchester United. Kawo yanzu Erling Haaland na Manchester City ya ci kwallo 12 a Champions League, shine kan gaba a wannan kwazon, Yayin da Vinicius Junior na Real Madrid keda shida a raga kawo yanzu. A kakar bara Real Madrid ta

Yan bindiga sun sace mutum 25 a wata majami'a a Kaduna

 Yan bindiga sun sace mutum 25 a wata majami'a a Kaduna   Wasu `yan bindiga sun kai hari kan wani Coci da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya inda suka sace mutum akalla 25.   Lamarin dai ya auku ne a ranar Lahadin da ta wuce lokacin da mutanen suke ibada a Cocin.   Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kaduna, Reverend John Hayap ya tabbatar wa BBC aukuwa lamarin inda ya ce mutum 40 aka sace kafin daga bisani mutum 15 sun kubuta.   Kakakin rundunar `yan sanda a jihar Kaduna, ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na AFP aukuwar lamarin amma bai yi karin bayani ba a kan batun.

Kotun zaɓen shugaban ƙasa ta ɗage zama zuwa Talata don jin ƙorafin PDP

  Kotun zaɓen shugaban ƙasa ta ɗage zama zuwa Talata don jin ƙorafin PDP Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya da ke zamanta a Abuja ta ɗage zamanta zuwa gobe Talata domin sauraron ƙorafin babbar jam'iyyar adawa ta PDP, da ɗan takararta Atiku Abubakar, da kuma jam'iyyar APM. Hukumar zaɓen ƙasar INEC ce ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri'a miliyan 8,794,726, bayan da ya kayar da manyan abokan takararsa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP. Bayan da suka yi watsi da sakamakon zaɓen Atiku da Obi sun nufi kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen don ƙalubalantar nasarar Tinubun. A zaman sauraron ƙorafe-ƙorafen da ta fara ranar Litinin, kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Haruna Tsammani ta alƙawarta yin adalci ga duka ɓangarorin da ke cikin shari'a.

Takarar Shugabancin Majalisar Dattawan Nijeriya Ta Fara Daukar Zafi, Inda Za A Fafata Tsakanin Abdul'aziz Yari Da Akpabio

Image
 Takarar Shugabancin Majalisar Dattawan Nijeriya Ta Fara Daukar Zafi, Inda Za A Fafata Tsakanin Abdul'aziz Yari Da Akpabio  Bayan anyi zaben shugaban kasa Allah ya bawa Bola Tinubu dake kudancin Najeriya Nasara, duk da kasancewar mu bamu goyi bayan shi ba kuma bamu zabe shi ba, amma hakan baisa ranmu ya baci ba ko kuma mu cigaba da yi mishi Adawa ko hassada ba, saboda mun tabbata haka Ubangiji ya kaddara bamu isa muyi jayayya ko fada da hukuncin Ubangiji ba.   A yanzu haka yankin Arewa ba tada wani wakilci mai karfi a cikin Gwamnatin Tarayya tunda ba tada shugaban kasa sai mataimakin shugaban kasa, shi kuma dama kusan kamar hoto ne a mulkin matukar ba shugaban kasa ne ya bashi dama a mulkin ba, kuma muna da sahihin labarin cewa Chief of Staff ma dan yankin kudu zasu bawa. Na tabbata mukamin shugaban majalisar dattawan Najeriya ne kadai yankin Arewa za ta samu domin ta rage radadin abubuwan da suke damunta, kuma a taimaki al-ummar Arewa da mukamin.   Mutane da dama basu san Capacity

Mutumin Da Ya Kashe Tsohuwar Matasar A Jihar Adamawa Saboda Ya Samu Labarin Za Ta Sake Wani Auren

Image
 Mutumin Da Ya Kashe Tsohuwar Matasar A Jihar Adamawa Saboda Ya Samu Labarin Za Ta Sake Wani Auren

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Hadarin Jirgin Ruwa Ya Ci Mutane Takwasa A Zamfara A Yayin Da Suka Je Nemawa Iyayensu Ruwan Sha Saboda Matsalar Ruwa Da Ake Fama Da Shi A Yankin

Image
 INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Hadarin Jirgin Ruwa Ya Ci Mutane Takwasa A Zamfara A Yayin Da Suka Je Nemawa Iyayensu Ruwan Sha Saboda Matsalar Ruwa Da Ake Fama Da Shi A Yankin A yau an samu faduwar jirgin ruwa a Gangaren Gulbi dake garin Gusau jihar Zamfara, inda aka samu asarar rayuwaka maza da mata wanda adadin su zai kai mutum takwas. Rahotanni sun nuna cewa mamatan sun je samowa iwayen su ruwan sha ne saboda matsalar ruwan sha da ya addabi cikin garin Gusau. Wadanda suka rasu Allah ya gafarta musu, Allah ya karbi shahadarsu.

Duk Sadda Na Tuna Cewa Na Ga Manzo Allah SAW A Cikin Mafarki, Na Kan Ji Zuciyata Ta Yi Fes, Cewar Sheikh Imam Mansoor

Image
 Duk Sadda Na Tuna Cewa Na Ga Manzo Allah SAW A Cikin Mafarki, Na Kan Ji Zuciyata Ta Yi Fes, Cewar Sheikh Imam Mansoor

Ina Rokon Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Idan Ya Karbi Mulki Ya Tamaka Ya Duba Maganar DCP Abba Kyari Saboda Muhimmancinsa Ga Kasa A Fannin Tsaro

Image
 Ina Rokon Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Idan Ya Karbi Mulki Ya Tamaka Ya Duba Maganar DCP Abba Kyari Saboda Muhimmancinsa Ga Kasa A Fannin Tsaro

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un 😭😭 yadda masu Ilimin kimiyya suka sawwara zanen wutar Jahannama take,

Image
 Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un 😭😭 yadda masu Ilimin kimiyya suka sawwara zanen wutar Jahannama take, wannan fa iya tunanin Dan Adam ne, Ballantana wutar Jahannama ta wuce hakan yadda suka sawwara ta 😭😭 Ya Allah kayi mana tsari da shiga wutar Jahannama 🤲😭

Kotu a Birtaniya za ta yanke wa Ekweremadu da matarsa hukunci a yau

Image
 Kotu a Birtaniya za ta yanke wa Ekweremadu da matarsa hukunci a yau   A yau ne kotun hukunta manyan laifuka ta Old Bailey da ke Birtaniya za ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa ​​Beatrice Ekweremadu da wani likita hukunci.   Wannan ya biyo bayan samun ɗan majalisar dattijan da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam a watan Maris.   Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da ɗan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda, inda ake sa ran yanke musu hukunci a karon farko a irin dokokin bauta ta zamani.   Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas.   An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London.   Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtan

Yan sanda sun kama matashin da ake zargi ya kashe mahaifiyarsa a Kano Kano

Image
 'Yan sanda sun kama matashin da ake zargi ya kashe mahaifiyarsa a Kano Kano Kano PoliceCopyright: Kano Police Rundura ƴan sanda a jihar Kano sun sanar da kama matashin nan Ibrahim Musa da ake zargi ya kashe mahaifiyarsa a Kano. A wani sako da kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an kama matashin ne a maɓoyarsa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa na jihar ta Kano. Kiyawa ya ce matashin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, inda kuma ya ce yana tu'ammali da ƙwayoyi masu sa maye. A yanzu dai za a tura shi zuwa kotu bayan kammala bincike. A jiya ne dai aka ruwaito cewa matashin ya caccaka wa mahaifiyarsa mai shekara 50 wuƙa a kanta da ƙirjinta da kuma sauran sassan jiki, inda ya tsere bayan aikata laifin.

2022: Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya a karon farko tun 1986 lokacin da ta ci a tare da Diego Maradona

Image
 🇦🇷 2022: Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya a karon farko tun 1986 lokacin da ta ci a tare da Diego Maradona  🇮🇹 2023: Napoli ta lashe Scudetto a karon farko tun 1987 lokacin da ta ci a tare da Diego Maradona  Mutuwar Maradona ta zama farin ciki ga Argentina da Napoli..... Sauran labarai shiganan: https://youtu.be/SahuWsQKQuU Daga: [Fagen Wasanni]

Yan Nijeriya 376 Aka Kwaso Daga Sudan, Cewar Minista Sadiya

Image
 'Yan Nijeriya 376 Aka Kwaso Daga Sudan, Cewar Minista Sadiya * Ba za mu bar ko mutum ɗaya a ƙasar ba, inji ta Jimillar 'yan Nijeriya 376 da su ka maƙale a ƙasar Sudan sun iso Abuja lafiya sakamakon aikin kwaso su da Gwamnatin Tarayya ke yi.  Mai ba da shawara ga Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Miss Nneka Anibeze, ita ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta ba manema labarai a ranar Alhamis. Ta ƙara da cewa kashin farko na mutanen da aka kwaso, wato mutum 94, sun sauka ne a daren ranar Laraba a jirgin Rundunar Mayaƙan Sama na Nijeriya samfurin Hercules C-130, yayin da sauran mutum 282 su ka sauka a jirgin kamfanin Air Peace.  Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta tsaya a filin jirgin sama na Abuja domin tarbar waɗanda aka ceto daga Sudan ɗin. A jawabin maraba da ta yi masu, ministar ta yi godiya ga Gwamnatin Tarayya saboda tattaunawar fahimtar juna da ta yi da gwamnatin Sudan wadda har ta kai ga samun karɓar &

Iyaye Mazauna G.R.A Ku Kula Sosai Masu Gadi Suna Korewa 'Ya'yanku Mazajen Aure, Domin Idan Mun Zo Hana Mu Shiga Suke

Image
 Iyaye Mazauna G.R.A Ku Kula Sosai Masu Gadi Suna Korewa 'Ya'yanku Mazajen Aure, Domin Idan Mun Zo Hana Mu Shiga Suke Daga M Najib Wambai, GML

SUBHANALLAH: Wani Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa A Kano

Image
 SUBHANALLAH: Wani Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa A Kano Wani matashi mai suna Ibrahim Musa, dan shekara 22, Mazaunin Unguwar Rimin Kebe dake Kano, ya yi amfani wuka wajen kashe mahaifiyarsa mai shekara 50, Hajara Muhammad.  Kakakin Rundunar 'yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Za mu ɓullo da matakan da za su hana alƙalai kwaɗayin cin hanci ba - Tinubu

Image
 Za mu ɓullo da matakan da za su hana alƙalai kwaɗayin cin hanci ba - Tinubu Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta samar da matakai da manufofin da za su sanya alƙalai da sauran ma'aikatan Najeriya daina kwaɗayin cin hanci. Tinubu wanda za a rantsar matsayin shugaban Najeriya nan da kwana 25 masu zuwa ya ce idan aka samar da matakan ƙarfafa gwiwa da suka dace, hakan zai tabbatar da kyakkyawan yanayin aiki da manufofi da za su sanya ma'aikata cikin sauƙi su iya samu rance don biyan buƙatun rayuwa. Hakan kuma zai rage kwaɗayin karɓar cin hanci da rashawa, in ji Tinubu. Wata sanarwa da wani jami'i a ofishin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Abdulaziz Abdulaziz ya fitar, ta ambato cewa Tinubu ya yi wannan alƙawari ne lokacin da yake ƙaddamar da rukunin gine-ginen kotun majistare ranar Alhamis a birnin Fatakwal na jihar Ribas. "Ba za ka yi tsammanin alƙalai su yi rayuwa a cikin yanayi maras kyawun gani ba. Wannan na cikin sauye-sauyen da suka wajaba a

Sojojin Nijeriya Sun Sake Ceto Wasu 'Yan Matan Chibok Guda Biyu Bayan Tsawon Shekaru Tara Suna Tsare A Hannun Boko Haram

Image
 Sojojin Nijeriya Sun Sake Ceto Wasu 'Yan Matan Chibok Guda Biyu Bayan Tsawon Shekaru Tara Suna Tsare A Hannun Boko Haram

Ɓarayi sun yi kuskuren sace takalma duka kafar dama a wani kanti

Image
 Ɓarayi sun yi kuskuren sace takalma duka kafar dama a wani kanti ... Getty ImagesCopyright: Getty Images Wasu ɓata-gari a ƙasar Peru sun yi rashin sa'a lokacin da suka je fashi a wani kantin sayar da takalma. Mutanen uku sun fasa kantin, wanda ke a tsakiyar birnin Huancayo kuma suka kwashe takalmi sawu-ciki sama da 200, sai dai dukkanin takalmin kafar dama ne. Mai kantin ya ƙiyasta cewa yawan takalmin da aka sace ya kai na kuɗi sama da dalar Amurka 13,000 duk da dai ɓarayin za su iya shan wahala kafin su iya sayar da su. Kyamarorin tsaro sun nuna yadda ɓarayin suka gudanar da fashin. Hotunan sun nuna yadda masu aikata laifin suka ɓalla kwaɗon shagon cikin tsakar dare sannan suka yi amfani da babur mai ƙafa uku wajen jigilar kwalaye maƙare da takalaman. Shugaban ƴan sandan yankin, Eduan Daiz ya shaida wa kafafen yaɗa labaran ƙasar ta Peru cewa "Mun tattara shaidu a wurin da lamarin ya faru, abin da ba a saba gani ba game da wannan fashin shi ne an sace takalman kafar dama kawa

Javier Tebas (Shugaban La Liga): "Idan Barcelonaa zata dawo da Leo Messi, zai kasance da karancin albashi fiye da yadda yake karba a PSG

Image
 Javier Tebas (Shugaban La Liga): "Idan Barcelonaa zata dawo da Leo Messi, zai kasance da karancin albashi fiye da yadda yake karba a PSG, kuma komawar sa yana da sharadi na siyar da 'yan wasa a kungiyar, kuma ina tsammanin Barcelona za ta sami adadi mai yawa daga siyar da 'yan wasa a wannan bazara." Daga: [Fagen Wasanni]

Ɗalibin Nijar ya rasu a hanyar komawa gida daga Sudan

Image
 Ɗalibin Nijar ya rasu a hanyar komawa gida daga Sudan ... Getty ImagesCopyright: Getty Images Wani ɗalibi ɗan ƙasar Nijar ya rasu a hanyar komawa gida daga Sudan bayan an kwaso su yayin da ake ci gaba da gwaɓza faɗa tsakanin sojojin gwamnati da kuma dakarun RSF. Ɗaya daga cikin wakilan ɗaliban, Ahmad Rabe Kani, ya ce ɗalibin ya rasu ne a kan hanya kafin su isa gida. Ya ce sun bar Sudan cikin ƙoshin lafiya tare da ɗalibin, amma da zuwan su Chadi sai ya yanke jiki ya faɗi. Ya ce a yanzu an isa Yamai da gawar ɗalibin domin yi masa jana'iza. Ɗaliban Nijar ɗin dai sun shafe tsawon kwanaki a Port Sudan kafin daga bisani su isa zuwa N'djamena da kuma komawa ƙasarsu ta wani jirgin soji. Ya ce su ɗaliban sun kai 45, inda ya ce akwai sauran mutum takwas a birnin Port Sudan.

Mutumin Da Yake Da Mata Huɗu Da Kuma 'Ya'ƴa 28, Ban Kuma Taɓa Sakin Mace Ba. Wannan Alama Ce Da Take Nuna Zan Iya Riƙe Shugabancin Majalisar Tarayya, Inji Alhassan Ado Doguwa

Image
 Mutumin Da Yake Da Mata Huɗu Da Kuma 'Ya'ƴa 28, Ban Kuma Taɓa Sakin Mace Ba. Wannan Alama Ce Da Take Nuna Zan Iya Riƙe Shugabancin Majalisar Tarayya, Inji Alhassan Ado Doguwa Daga Abubakar Shehu Dokoki

Hanya daya cikin gaggawa da Manchester City zata iya ragargaza Real Madrid a wasan kusa dana karshe....

Image
 Hanya daya cikin gaggawa da Manchester City zata iya ragargaza Real Madrid a wasan kusa dana karshe.... Shin kun yarda kuwa🤣🤣

Yan wasa mafi zura kwallaye a kakar wasa guda daya a manyan Lig-Lig guda biyar na Turai:

Image
 'Yan wasa mafi zura kwallaye a kakar wasa guda daya a manyan Lig-Lig guda biyar na Turai: 50- La Liga - Leo Messi  35* - EPL - Haaland 36 - Serie A - Ciro Immobile 41 - Bundesliga - Lewandowski 44- Ligue 1 - Josip Skoblar Daga: [Fagen Wasanni]

Mashaƙo ta kashe mutum 73 a Najeriya - WHO

Image
  Mashaƙo ta kashe mutum 73 a Najeriya - WHO Getty Images Copyright: Getty Images Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce mashaƙo ta kashe mutum 73 yayin da 557 kuma suka kamu da cutar tun fara wannan shekara. A wani rahoto da hukumar ta fitar a jiya Laraba, ta ce an samu ɓarkewar cutar a jihohi 21 na Najeriya. Mashaƙo dai wata cuta ce da ke kama yara waɗanda suka kai shekara biyar da kuma manya da suka haura shekara 60. WHO ta ce an fi samun yawan alkaluman waɗand suka kamu da cutar ce a jihar Kano, inda mutum 1,118 suka kamu, sai Yobe mai 97 da Katsina mai mutum 61 da suka kamu da Legas mai 25, sai Sokoto mutum 14 da kuma Zamfara mai mutum 13. Rahoton ya ce daga ranar 14 ga watan Mayun 2022 zuwa 9 ga watan Afrilun 2023, an samu alkaluman mutum 1, 439 da ake zargin sun kamu da cutar ta mashaƙo, inda cutar ta yi sanadiyyar rayuka 73.

Buhari ya Mayar da Najeriya baya shekaru “100” sai jajurtaccen shugaba kaɗai zai iya dawo da ita yadda take, Buba Galadima.

Image
 Buhari ya Mayar da Najeriya baya shekaru “100” sai jajurtaccen shugaba kaɗai zai iya dawo da ita yadda take, Buba Galadima.

Manchester City 2 - 0 West Ham United Nathan Ake ⚽ Erling Haaland

Image
 82' Manchester City 2 - 0 West Ham United  Nathan Ake ⚽  Erling Haaland  83' Liverpool 1-0 Full Ham Salah ⚽ #labaran kullum #PremierLeague #PremierLeagueLive

Burina Na Samu Miji Nagari Jajirtacce Domin Gina Rayuwa Mai Inganci, Cewar Matashiya Mai Baiwar Gemu

Image
 Burina Na Samu Miji Nagari Jajirtacce Domin Gina Rayuwa Mai Inganci, Cewar Matashiya Mai Baiwar Gemu Matashiyar mai suna Aïcha Kanté, ta kuma kara da cewa tana alfahari da irin baiwar da Allah ya yi mata na zama maccen da ke da baiwa irin wannan wannan.

ABIN MAMAKI: Magoya bayan Paris sun je gidan Neymar domin neman ya bar kungiyar ta PSG!

Image
 ABIN MAMAKI: Magoya bayan Paris sun je gidan Neymar domin neman ya bar kungiyar ta PSG! 

MASÙ SAÑ AURE NÀ: Zan Aureka Idañ Ka Cikà Dukkan Waɗannan Sharuɗan, Safara'u Ta Gindaya Tsauraran Sharuɗɗa Ga Masu Son Aurenta

Image
 MASÙ SAÑ AURE NÀ: Zan Aureka Idañ Ka Cikà Dukkan Waɗannan Sharuɗan, Safara'u Ta Gindaya Tsauraran Sharuɗɗa Ga Masu Son Aurenta Shaharriyar ƴar Kannywood kuma mawaƙiyar nan Safara'u Yusuf (Safaa), ta gindaya wasu tsaurarn sharuɗa ga duk wanda yake da buƙatar don aurenta. Na farko dole mu yi yarjejeniya a rubuce kasa hannu nima in sa, cewar bayan ka aureni za ka barni in cigaba da sana'a ta wato rawa da waƙa. Na biyu idan ba za ka barni ba to za ka bani jarin naira miliyan 100 domin in fara zuwa Dubai ina siyo kaya ina siyarwa. Na uku dole ka bani kyautar gida a Kaduna da Abuja da kuma motar hawa wacce ta kai darajar naira miliyan 15. Idan ka ga za ka iya to ka ajiye min number wayarka zan kira ka. Mè Zakù Cè ?

Na Haɗu Da Wata Ƴar Ƙasar Chana Jiya, Har Mun Fara Maganar Aure, Ya Ku Ke Gani? Ku Ba Ni Shawara, Cewar Jarumin Fina-finan Hausa, Adam A. Zango

Image
 Na Haɗu Da Wata Ƴar Ƙasar Chana Jiya, Har Mun Fara Maganar Aure, Ya Ku Ke Gani? Ku Ba Ni Shawara, Cewar Jarumin Fina-finan Hausa, Adam A. Zango

Bayan Kwashe Shekara 32 Da Yin Aure, Ba Su Taɓa Haihuwa Ba, Allah Ya Albarkace Su Da Haihuwar Ƴan Biyu Mace Da Namiji

Image
 Bayan Kwashe Shekara 32 Da Yin Aure, Ba Su Taɓa Haihuwa Ba, Allah Ya Albarkace Su Da Haihuwar Ƴan Biyu Mace Da Namiji Allah Ya Raya!

FT: Juventus 2-1 Lecce. Nasara ta farko a wasanni 6. Juventus ta koma matsayi na 2 a teburin gasar Seria A yanzu.

Image
 FT: Juventus 2-1 Lecce.  Nasara ta farko a wasanni 6. Juventus ta koma matsayi na 2 a teburin gasar Seria A yanzu.

Anyikira Ga Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Ya Bawa Yari Shugaban Majalisar Dattawa

Image
 Anyikira Ga Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Ya Bawa Yari Shugaban Majalisar Dattawa. Kungiyar siyasa a arewa maso yammacin Najeriya ta nemi zababben shugaban kasa da ya bai wa Abdulazizi Yari shugabancin Majalisar Dattawa. Ƙungiyar mai suna 'The North-West Progressives Forum' ta gargadi zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu da kada ya kuskura ya ba da dama ga sauran yankunan kasar na shugabancin majalisar. 1 Kungiyar Arewa ta NPF ta ce Yari ne ya fi dacewa da zama shugaban majalisa ta 10.  Shugaban kungiyar, Nasir Danbatta da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a ranar Asabar 29 ga watan Afrilu, yace arewa maso yammacin kasar tafi kowane yanki ba da ƙuri'u wa jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa da ya gabata. Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kungiyar dake arewa maso yamma tace babu wanda ya cancanci kujerar majalisar dattawa kamar tsohon gwamnan Zamfara.  Idan za a yi adalci, a ba Yari shugabancin majalisa Ta kuma gargadi zababben shugana kasar Najeriya da ya tabbatar ya ba

Magoya bayan PSG sunyi dafifi a sansanin kungiyar suna rera wakokin kalaman batanci ga Leo Messi.

Image
 Magoya bayan PSG sunyi dafifi a sansanin kungiyar suna rera wakokin kalaman batanci ga Leo Messi.